A ranar Juma’a za a kammala buga wasannin zagayen farko na gasar cin kofin duniya da ake fafatawa a Qatar.
Kawo yanzu wasu kasashen sun tsallake zuwa zagaye na biyu wasu kuma an fitar da su. In ji BBC.
A yayin da akwai wasu karin kasashen da suma za su iya kaiwa mataki na gaba.
Rukunin A
A wannan rukunin kasashen Netherlands da Senegal su ne za su buga wasanni a zagaye na biyu.
A yayin da mai masaukin baki Qatar da Ecuador kuma aka fitar da su.
Rukunin B
Ingila da Amurka su ne suka haye zuwa mataki na gaba a yayin da Iran da Wales kuma aka fitar da su.
Rukunin C
Argentina da Poland su ne kasashen da suka yi nasarar tsallakewa zuwa mataki na gaba a gasar.
A yayin da Saudi Arabiya da kuma Mexico suka fita daga cikin gasar.
Rukunin D
Faransa da Australiya su ne kasashe biyu da suka fito daga wannan rukunin duk da cewa Tunisia ta doke Faransar a wasansu na karshe.
Denmark da Tunisia su ne suka gamu da rashin sa’a a wannan rukunin.
Rukunin E
Spaniya da Costa Rica da Japan da kuma Jamus su ne a wannan rukunin. Amma kawo yanzu babu wacce ta tsallake zuwa zagaye na biyu. Sai a wasanninsu na yau za a sani.
Spaniya za ta kara da Japan sai kuma Jamus ta hadu da Costa Rica.
Rukunin F
Croatia da Belgium da Canada da Morocco su ne a wannan rukunin.
Canada ta riga ta san makomarta saboda an doke ta a wasanni biyu na farko saboda haka ba za ta kai zagaye na gaba ba.
Rukunin G
Brazil ta tsallake zuwa zagaye na biyu.
Sai dai a ranar Juma’a za a san tsakanin Switzerland da Kamaru da Serbiya kasar da za ta kai mataki na gaba.
Rukunin H
Portugal ta kai matakin zagaye na biyu a gasar bayan ta samu nasara a wasanni biyu a jere.
Ghana da Koriya ta Kudu da Uruguay su ne sauran kasashen da ke a rukunin kuma a cikinsu kasa daya ce za ta iya kai wa mataki na gaba.
Kasashe 16 ne za su kai mataki na biyu a gasar cin kofin duniya.