Ƙasashen Afrika 17 sun kauce wa jefa ƙuri’a a Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) don yin Allah wadai da hare-haren Rasha a kan Ukraine.
Daga cikin ƙasashen da ba su kaɗa ƙuri’ar ba akwai Afirka ta Kudu, da Aljeriya, da Uganda, da Burundi, da Senegal, da Sudan ta Kudu, da Mali, da kuma Mozambique.
Sauran su ne: Sudan, Namibia, Angola, Zimbabwe, Equatorial Guinea, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Madagascar, Tanzania da Congo.
Eritrea ce ƙasar Afirka kaɗai da ta kaɗa ƙuri’ar ƙin amincewa da ƙudirin na sukar matakin Rasha.
Uganda ta ce ta ƙi kaɗa ƙuri’ar ne saboda ta ci gaba da tabbatar da matsayinta na “yar ba-ruwana” yayin da take ƙoƙarin zama shugabar gamayyar ƙasashe ‘yan ba-ruwana ta Non-Aligned Movement (Nam). In ji BBC.