fidelitybank

Ƙasa ta danne masu haƙar ma’adanai 30 a Abuja

Date:

Masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba 30 ne suka mutu, bayan ƙasa ta rufta kansu a ƙaramar hukumar Kuje da ke Abuja.

Shugaban ƙaramar hukumar ne ya bayyana haka ranar Alhamis, a lokacin da shugabannin ƙananan hukumomin birnin suka gana da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Haka kuma masu garkuwa da mutane sun sace mutum 19 ranar Alhamis a yankin ƙaramar hukumar Bwari da ke Abuja.

Ministan wanda ya nuna damuwarsa game da waɗannan batutuwa – ya ce zai gayyaci daraktan hukumar tsaron farin kaya da kwamishinan ‘yan sanda birnin domin ɗaukar matakan da suka dace don kuɓutar da mutanen.

Mista Wike ya kuma yi kira ga shugabannin ƙananan hukumomin da su kafa kwamitocin sa ido a ƙananan hukumominsu domin lura da ayyukan masu haƙar ma’adinai.

Ya kuma ce a nasa ɓangare zai gana da ministan ma’adinai Dele Alake domin kawo ƙarshen ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Abuja.

jalingo news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp