fidelitybank

Ƙarya ne mu na baiwa Ɗaurarun Kano abinci – Hukumar Gidajen Yari

Date:

Hukumar Kula da Gidajen Yarin Najeriya reshen jihar Kano, ta musanta rahotonnin da wasu kafofin yaɗa labarai suka ruwaito na rashin bai wa fursunonin da ke ɗaure a gidajen yarin jihar wadataccen abinci.

A baya-baya nan dai an yi ta samun labaran ƙorafe-ƙorafe kan rashin bai wa fursunonin wadataccen abinci a jihar a shafukan sada zumunta.

To sai dai cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da gidajen yarin jihar, Musbahu Lawan K/Nasarawa ya fitar ya ce, an yaɗa rahotonni ne kawai domin ɓata wa hukumarsu suna.

”Waɗannan rahotonni abin takaici ne, kuma hukumarmu na shaida wa al’umma cewa walwala da jin daɗin fusunoninmu shi ne babban abin da hukumarmu ta sanya a gaba, don haka ne koyaushe hukumarmu ke tabbatar wannan muradi duk kuwa da halin matsin tattalin arziki da ƙarsamu ke ciki”, in ji sanarwar.

Ya kuma ƙara da cewa ba abinci kawai hukumar hukumar ke bai wa fursunonin ba, har ma da ilimantar da su da kuma ba su horon sana’o’in dogaro da kai da za su taimaki rayuwarsu bayan kammala zaman gidan yarin.

A Najeriya ana yawan samun ƙorafe-ƙorafe kan halin da ɗaurarru ke ciki a gidajen yarin ƙasar, kama daga kula da lafiyarsu da abinci da kuma babbar matsalar cunkoson fursunoni a gidajen yarin.

the punch newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp