fidelitybank

Ƙarin farashin litar mai zai jefa ma’aikata talauci – TUC

Date:

Ƙungiyar ƙwadago ta TUC, ta yi gargaɗin cewa, matakin ƙarin kuɗin man fetur da NNPCL ta yi zai ƙara jefa ma’aikata cikin matsanancin talauci.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, shugaban kungiyar ta TUC, Kwamared Festus Osifo, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta janye matakin ƙarin kuɗin.

”Maimakon hakan gwamnati ta aiwatar da tsare-tsare da zai ƙarfafa kuɗin ƙasarmu, da kuma ɗaukar ƙwararan matakai domin sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya raɗaɗin talaucin da suke ciki”, in ji sanarwar.

Kungiyar ta ce ya kamata a ɗauki irin wannan mataki ba tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki ba, inda ta bayyana hakan a matsayin rashin mutunta jin daɗin ‘yan Najeriya, musamman ma’aikata, waɗanda irin waɗannan manufofin suka fi shafa.

Osifo ya ƙara jaddada cewa “hauhawar farashin man fetur da wutar lantarki zai ƙara dagula ƙalubalen da ake fuskanta, wanda zai haifar da ƙarin wahalhalu da tashin hankali.”

“Ya kamata a ɗauki matakin gaggawa don maido da ƙwarin gwiwar jama’a da kuma hana ci gaba da taɓarɓarewar rayuwar ‘yan ƙasa,” inji shi.

vanguardnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp