fidelitybank

Ƙarfe 6 za a fara zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa a faɗi sakamako ƙarfe 10 – APC

Date:

A yau ne da karfe 6 na yamma za a fara zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a babban taron jam’iyyar na kasa a Abuja.

Kamar yadda jadawalin ya nuna, ana sa ran wakilan da suka cancanta daga jihohin kasar nan 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja, za su isa wurin da misalin karfe 10 na safe zuwa karfe 1 na rana.

Wurin da za a gudanar da babban taron jam’iyyar APC na kasa a dandalin Eagle Square dake Abuja.

Jadawalin taron da jam’iyyar ta fitar, ya nuna cewa shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Adamu zai gabatar da jawabin maraba da misalin karfe 3:40 na rana.

A halin da ake ciki, za a bar masu neman shugabancin kasar su gabatar da jawabansu tsakanin karfe 4:45 na yamma zuwa 5:45 na yamma.

Buhari zai gabatar da jawabinsa da karfe 5:45 na yamma. Wakilan za su fara kada kuri’a daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 9 na yamma, yayin da za a bayyana sakamakon da karfe 10 na dare.

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp