Dan wasan gaba na Chelsea, Timo Werner ya sauka a Jamus don kammala komawa RB Leipzig.
Werner na shirin komawa kulob din Bundesliga shekaru biyu bayan ya tafi Stamford Bridge.
Timo Werner ya sauka a Leipzig domin a duba lafiyarsa sannan kuma ya sanya hannu kan kwantiragi a matsayin sabon dan wasan RB Leipzig, yana tare da wakilansa yayin da Chelsea ta amince da yarjejeniyar.
“Chelsea za ta karɓi ƙayyadaddun farashin ɗan miliyan 20 da ƙari. Šeško zai sanya hannu a yanzu amma don 2023, ”in ji Fabrizio Romano, masani kan harkar kwallon kafa.
A halin yanzu, Arsenal ta sanar da sayar da Lucas Torreira ga Galatasaray.
Dan wasan tsakiya na Uruguay ya koma Turkiyya a kan kudi fam miliyan 5.5, inda ya kulla kwantiragin shekaru hudu da sabon kulob din.