Dan takarar shugabancin ƙasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Muhammad Hayatu-Deen ya janye daga takarar shugabanci.
Tsohon shugaban bankin FSB ya bayyana hakan ne cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na kasa Dr Iyorchia Ayu.
Hayatu-Deen ya fice daga takarar ne kwana guda bayan da tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi ya sanar da janyewarsa daga takarar tare da ficewa gaba daya daga jam’iyyar ta PDP baki daya.
Ba kamar Obi ba, Hayatu-Deen ya ce zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar ta su.