Hukumar zaɓe ta ayyana ɗan takarar gwamnan jihar kebbi ƙarƙashin jam’iyyar APC, Nasiru Idris, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka ƙarasa ranar Asabar 15 ga watan Afrilu.
Jami’in tattara sakamakon zaɓen Farfesa Yusuf Saidu na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ya ce Nariru Idris na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’a 409,225.
Inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya wanda ya samu ƙuri’a 360,940.
Sakamakon zaɓen ya nuna cewa Nasiru Idris ya samu nasara da tazarar ƙuri’a 48,285.
Zaɓen gwamnan jihar Kebbi na daga cikin zaɓukan gwamnonin jihohin da hukumar zaɓe ta ce, ba su kammala ba a zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris.


