fidelitybank

Ɗan sanda na neman kotu ta rusa aurensa bisa zargin matarsa da bin maza

Date:

Wani ɗan sanda, Rafiu Ademola ɗan shekara 45 ya roƙi kotu a Igando da ta rusa aurensa da matarsa a bisa zargin ta na bin maza.

Ɗan sandan ya shaidawa kotun cewa mai-ɗakin nasa ta zama karya.

Ya kuma koka da cewa shi da idonsa ya ga irin zantukan batsa da matarsa ke yi da maza daban-daban ta WhatsApp da kuma guraren da su ke haɗuwa.

“A cikin saƙonnin da na gani har da wanda ta cewa wai ba ta da aure kuma wai a gidan yayarta ta ke zaune.

“na aika duka hirarrakin zuwa waya ta domin ya zame mini shaida,” Ademola ya shaidawa kotun.

Mai ƙarar ya ƙara da cewa matar tasa ta fiye son jiki kuma ba ta don yin girki a gidan kuma ba ta girmama mahaifansa.

A ƙarshe dai ɗan sandan ya shaidawa kotun cewa shifa yanzu ba ya son matar ta sa, inda ya roƙi kotun da ta datse igiyar auren nasu.

A na ta ɓangaren, Rashidat ta musanta duk zarge-zargen da mijin nata ya yi a kotun, amma kuma ta amince da a yanke auren.

“Ni ban taɓa bin maza ba , shine ma yanke bin mata iri-iri har ya na kawo mata cikin gidan mu na aure.

“Kwanan nan ya kore ni da ga gidan ya riƙa kuma kawo mata su na kwana a gidan,” in ji ta.

Rashidat, ƴar shekara 40 kuma mai sana’ar telanci ta shaidawa kotun cewa mijin nata ya maida ita jaka, inda ya ke jibagrta a duk sanda ya ga dama.

Kotun, wacce ta ke ƙarƙashin alƙali Adeniyi Koledoye, ya yi kira ga ma’auratan da su zauna lafiya, inda ya ɗaga zaman zuwa 16 ga watan Disamba domin yanke hukunci.

legit news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp