fidelitybank

Ƴanbindiga sun kashe tare da sace kuɗaɗe a wani hari a Kebbi

Date:

Hukumomi da ga jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum guda tare da raunata wasu bayan da wasu ƴanbindiga suka kai hari garin Gulma da ke yankin aramar hukumar Argungu a jihar.

Shugaban ƙaramar hukumar Hon Aliyu Sani Gulma, ya shaida wa BBC cewa maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe takwas na maraicen ranar Alhamis ɗaue da muggan makamai.

”Ƴanbindigar sun shiga garin ne a kan babura bakwai ɗauke da goyon bibbiyu, ciki har da mata biyu, ɗauke da muggan makamai, inda suka je wani babban kantin sayar da kayyaki na Alh Fatawu a garin, suka kuma buƙaci a ba su kuɗaɗe”.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce mata biyu daga cikin ƴanbindigar sun tsaya a ƙofar kantin, riƙe da bindigogi, yayin da sauran mazan suka shiga cikin domin ƙwato kuɗaɗe.

”Sun faɗa masu kantin cewa kuɗin Saifa suke ce ba naira ba, sa dai kuma a kantin babu saifar sosai, lamarin da ya sa suka riƙa bugun masu kula da kantin, inda daga baya suka kwashe duka kuɗaɗen da ke cikin kantin suka yi awon gaba da su”, a cewar shuagaban ƙaramar hukumar.

Ya ce maharan sun kuma kashe mutum guda a cikin al’ummar gari tare da raunata wasu a dama a lokacin da suka shiga garin.

legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp