Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta tabbatar da kai wani hari kan wasu jami’an ƙungiyar tsaro ta Community Watch Corps a jihar, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 25.
Lamarin ya faru ne ranar Laraba lokacin da jami’an tsaron na Community Watch Corps, suka yi zango a garin Ɓaure na jihar ta Katsina, bayan ziyarar ta’aziyar ɗaya daga cikin abokin aikinsu da ya mutu sakamakon harin ’yanbindigar.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka shida lamarin ya shaida wa BBC cewa kwantan ɓunar-da ‘yanbindigar suka yi wa jami’an ya janyo mutuwar fiye jami’an na Community Watch Corps 10.
‘’Bayan sun tsaya ne, sai kwatsam ‘yanbindigar suka buɗe musu wuta, kuma sun kashe aƙalla mutum 15’’, in ji shi.
Ya kuma ce bayan kashe mutanen ‘yanbidigar sun hana a ɗauki gawarwakinsu har sai ranar Alhamis da safe.
Bayan kashe jami’an tsaron na ‘Community Watch Corps’, mutanen gari sun fantsama kasancewar ranar kasuwar gari ne, lamarin da ya sa aka kashe wasu daga cikinsu, inda har yanzu ba a ga wasu mutanen ba kamar yadda wasu mazauna yankin suka bayyana wa BBC.
‘’Sun kashe mutanen ƙauyukan yankin masu yawa, aƙalla mutanen da suka kashe sun kai mutum 25’’, a cewar wani da ya shaida lamarin.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Katsina,Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, sai dai ya ce suka ci gaba da tattara bayanai.
Yankunan ƙananan hukmomin Safana da Batsari na daga cikin yankunan jihar Katsina masu mafa da matsalar tsaro.