Akalla ‘yan takarar kujerar gwamna guda shida da ‘yan takarar Sanata tara ne ke neman tikitin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party a Filato.
Shugaban NNPP na Filato, Tokji Mandim, wanda ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a ranar Litinin, a Jos, ya ce jam’iyyar za ta tsayar da ‘yan takara a dukkan mukamai da za a yi a jihar.
Mandim ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa cewa, za a gudanar da zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar ne a ranar Talata a Jos yayin da na Majalisar Dattawa, Wakilai, da na Majalisar Dokoki za su gudana a cikin mako guda.