Ƙungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) ta bayyana goyon bayanta ga Falasdinawa sakamakon rikicin da ya barke tsakanin su Isra’ila.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tattakin, wanda ya fara da misalin karfe 4 na yammacin ranar Litinin daga Banex Plaza Abuja, ya kare ne a kan titin Ahmadu Bello.
A cikin wata sanarwa da dan kungiyar Sheikh Sidi Munir Sokoto ya fitar, ya ce: “Mun samu kanmu a wata hanyar da ba za mu iya guje wa ba, an daure mu da riga guda daya ta kaddara. Duk abin da ya shafi ɓangare ɗaya kai tsaye, yana shafar kowa da kowa”.
Rikicin da ke da nasaba da hare-haren da aka kai a masallacin al-Aqsa da kuma sansanin ‘yan gudun hijira na Gaza a shekarun da suka gabata, ya haifar da asarar rayuka fiye da 1,000 daga bangarorin biyu.