Rundunar ‘yan sanda reshen Jihar Osun, ta ce, ta kama mutum biyar da ake zargi da kai wa ayarin motocin matar Gwamnan Osun, Kafayat Oyetola, hari a ranar Juma’a da dare.
A cewar sanarwar da kakakin rundunar, Yemisi Opalola, ta fitar, lamarin ya faru ne lokacin da wani direban babbar mota ya rufe hanya.
Rahotanni sun ce, jami’an tsaron da ke tare da matar gwamnan sun ji raunuka daban-daban lokacin da ‘yan bindiga suka buɗe musu wuta a yankin Owode Ede yayin da take kan hanyar koma wa Osogbo, babban birnin jihar.
Wata mazauniyar yankin ta shaidawa manema labarai cewa wata motar dakon kaya ce ta soma haddasa cunkoson ababben hawa lokacin da ayarin motocin matar gwamnan suka iso kasuwar Owode.
A cewarta, a wannan lokaci aka buɗe wuta, aka dinga harbe-harbe kan motocin.


