Rahotanni sun bayyana cewa, an hallaka wani kasurgumin ɗan bindiga mai suna Yellow, wanda ake zargin shi da ’yan dabansa su na addabar yankuna da dama a jihohin Neja da Zamfara da kuma Kebbi.
An dai halaka jagoran ‘yan bindigan ne da wasu mukarrabansa akalla uku a wani karon battar da su ka yi da jami’an tsaro a tsakar daren jiya, a garin Wasagu na jihar Kebbi.