Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Imo, sun cafke wani da ake zargin dan kungiyar tsaro ta Eastern Security Network, ESN, Simeon Onigbo da ake zargi da kera bama-bamai ga kungiyar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Mike Abattam, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu a madadin kwamishinan ‘yan sandan, Mohammed Barde, ya ce, wanda ake zargin ya amince da aikata laifin tare da yin alkawarin bayyana maboyar ‘yan ta’addan.
Sanarwar ta yi zargin cewa Onigbo ya kasance yana samar da bama-bamai da aka kera a cikin gida da ake amfani da su wajen kai hare-hare a sassan ‘yan sanda da sauran cibiyoyin gwamnati a Imo.