fidelitybank

Ƴan Sanda sun cafke ɗan fashin daji mai shekara 20 da haihuwa a Zamfara

Date:

 

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Zamfara ta tabbatar da cafke wani ƙasurgumin ɗan fashin daji, Sani Mati, wanda a ka fi sani da Mai-ƴanmata a jihar.
Rundunar ta ce Mai-ƴanmata, ɗan shekara 20 kacal da haihuwa, ya ƙware wajen garkuwa da mutane, fashin daji, satar shanu da sauran manyan laifuka a yankin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji a Zamfara.
Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar Zamfara, Ayuba N. Elkanah ne ya baiyana haka a taron manema labarai yayin da rundunar ta yi holon ɗan ta’addan a juya Laraba.
A cewar Kwamishinan, ” a ranar 28 ga Disamba da misalin ƙarfe 5 na yamma, yayin da su ke wani sintiri na sirri bayan sun samu bayanan sirri, sun cafke wani ƙasurgumin ɗan fashin daji mai suna Sani Mati, wanda a ka fi sani da Mai-ƴanmata ɗan ƙauyen Mayasa a Ƙaramar Hukumar Zurmi.
Ya ƙara da cewa Mai-ƴanmata ya shiga komar ƴan sanadan ne lokacin yana shirin sanya shinge ya tsare bayin Allah domin ya yi garkuwa da su a daidai wani ƙauye mai suna Koliya.
Elkanah ya ƙara da cewa da a ɓangaren Turji Mai-ƴanmata ya ke, inda yanzu ya koma sansanin wani ƙasurgumin ɗan fashin daji mai suna Kachalla Sani Black.
Ya ce an samu bindiga samfurin AK-47, sai kwanson harsashi 2, sai harsashi 3 da kuma babur guda 1.
Ya ce a na nan a na yi masa tambayoyi inda da ga nan za a ki shi kotu.

@nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp