Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya tare da hadin gwiwar ‘yan sandan Interpol, sun kwato wasu motoci da aka sace a Najeriya daga Jamhuriyar Nijar.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ranar Juma’a, ta ce, “Sufeto-janar na ‘yan sandan, Usman Baba, ya yaba da hadin kai da hadin gwiwa tsakanin kasashe 194 na kungiyar ‘yan sanda ta kasa da kasa mai yaki da miyagun laifuka, wanda ya taimaka wa ‘yan sandan hadin gwiwa a duniya baki daya.
“IGP din ya kuma yaba wa jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta ‘yan sanda, Interpol, saboda yadda suka yi amfani da dandalin da aka samar ta hanyar INTERPOL, domin dakile laifukan da suka shafi kan iyaka, musamman laifukan da suka shiga wasu kasashen Afrika da ke makwabtaka da su.
Ya yi wannan tsokaci ne a kan nasarar kwato motoci uku da aka sace daga Najeriya a Jamhuriyar Nijar.