Dubban mutane ne suka gudanar da maci ranar Alhamis a Niamey, babban birnin Nijar don nuna goyon baya ga juyin mulkin da ya kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin dimokraɗiyya.
Ana zanga-zangar ne yayin da damuwar da ake ita game da tsaro ke ƙaruwa a tsakanin ƙasashen Yamma.
Masu zanga-zanga a tsakiyar birnin Niamey, wasunsu na kaɗa manyan tutocin Rasha, suna rera taken ƙin jinin Faransa a lokacin gangamin, wanda aka kira don bikin samun ‘yancin kan ƙasar daga tsohuwar uwargijiyarta Faransa a 1960.
Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula na Nijar sun yi kira ga al’ummar ƙasar su yi watsi da takunkuman karya tattalin arziƙi da Ecowas ta sanya wa Nijar.
Ƙungiyar Ecowas dai ta ce za ta yi amfani da ƙarfin soji matuƙar masu juyin mulkin ba su mayar da Bazoum kan karagar mulki ba.
Duk da wannan nuna goyon baya da fararen hula ke yi wa sojojin, akwai ‘yan Nijar masu yawa da ke adawa da juyin mulkin.
Wasu na zargin cewa sosjojin ne suka kitsa zanga-zangar domin gudun kawar da su daga kan mulki.
To amma yanzu a ƙoƙarinsu na kafa hujja kan juyin mulkin, sojojin na yunƙurin harzuƙa batun ƙin jinin Faransa.
Abin da kuma ya faru kenan a Mali da Burkina Faso, inda jagororin mulkin sojin ke ƙara ƙulla ƙawance da Rasha.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa ɗaruruwan matasan riƙe da tutocin ƙasar Rasha sun taru a dandalin samun ‘yanci da ke tsakiyar birnin Yamai.
Issiaka Hamadou ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ya ce ”magana ce a kan matsalar tsaro, muna buƙatar taimakon sojoji, kuma muna maraba da shi daga ko’ina ne ba lallai sai Rasha kaɗai ba, ko China ko Turkiyya ne, matuƙar za su taimaka mana”.
“Ba ma son Faransa, waɗanda ke sace mana ma’adanai, tun cikin 1960 suke nan kuma babu abin da ya sauya”, in ji shi.
Faransa na da dakarun soji kimanin 1,500 a Nijar a yaƙin da suke yi da masu iƙirarin jihadi na yankin Sahel.
“Na kasa samun aiki bayan kammala karatu a ƙasar nan, saboda gwamnatin Bazoum da ke samun goyon bayan Faransa,” in ji wani matashi da ya bayyana sunansa da Oumar.
Masu goyon bayan gwamnatin sojin ƙasar na cewa Faransa ta kasa magance musu matsalar masu iƙirarin jihadi, yayin da suke ganin Rasha ce ta fi cancanta da ƙulla ƙawance. A cewar BBC.