Akalla ‘yan Najeriya 174 da suka makale sun dawo daga kasar Libya, a cewar jami’an agajin gaggawa a ranar Laraba.
Gidan Talabijin na Channels ta tattaro cewa, sabbin mutanen da suka dawo sun isa bangaren dakon kaya na filin jirgin saman Murtala Muhammed International Airport (MMIA) da misalin karfe 3:35 na yammacin ranar Talata. Sun kunshi mata 84 da maza 90.
Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Habib Ahmed, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an dawo da mutanen ne a cikin jirgin Al Buraq Air Boeing 737-800.
Shugaban hukumar ta NEMA wanda ya samu wakilcin kodinetan ofishin hukumar na Legas, Ibrahim Farinloye, ya ce akwai manya maza 75 da yara maza 12 da jarirai maza uku a cikin jirgin.
“Bayanan mutanen da suka dawo sun nuna cewa an dawo da manya mata 69, yara mata biyar da jarirai mata 10. Haka kuma a cikin jirgin akwai manya maza 75, yara maza 12 da jarirai maza uku,” in ji sanarwar.
“A cikin wadanda aka dawo da su akwai 23 da ke da kananan cututtukan. Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa (IOM) tare da hadin gwiwar kungiyar tarayyar turai ta fara kwaso dubunnan ‘yan Najeriya da suka makale daga kasashe daban-daban tun daga shekarar 2017 ta hanyar wani shiri na musamman na taimaka wa ‘yan gudun hijira.
“A wannan shekarar kadai, jirgin na yau ya zama na 12 da aka rubuta a karshen atisayen a Legas. A dunkule, kimanin ‘yan Najeriya 2,044 da suka dawo daga kasar Libya ne aka dawo da su kasar ta filin jirgin Murtala Muhammad dake Ikeja.
“A cikin wadanda aka dawo da su akwai 23 da ke da kananan cututtukan. Hukumar kula da ‘yan ci-rani ta duniya (IOM) tare da hadin gwiwar kungiyar Tarayyar Turai sun fara kwaso dubunnan ‘yan Najeriya da suka makale daga kasashe daban-daban tun daga shekarar 2017 ta hanyar wani shiri na musamman na taimaka wa ‘yan gudun hijira.
“A wannan shekarar kadai, jirgin na yau ya zama na 12 da aka rubuta a karshen atisayen a Legas. A dunkule, kimanin ‘yan Najeriya 2,044 da suka dawo daga kasar Libya ne aka dawo da su kasar ta filin jirgin Murtala Muhammad dake Ikeja.
“Mutane 2,044 sun hada da manya maza 848, manya mata 719, yara 180 da jarirai 123 sun dawo ta hanyar MMIA a bana.”


