fidelitybank

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Date:

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa a ƙirji da ’yan daba suka yi a kofar gidan tsohon shugaban karamar hukumar Dala, Ibrahim Dan Isle, da ke Bachirawa, titin Sakatariya, layin Dan Isle.

Arewa Update ta rawaito cewa, Dan uwan marigayin, Abubakar Mahmud, ya shaida wa Arewa Updates cewa Ibrahim mabiyin tsohon shugaban karamar hukumar ne a siyasa, daga baya suka ɓaɓe, sai a baya-bayan nan suka shirya.

Ya ce Dan Islen ne ya gayyace shi gida domin karɓar naman Sallah, kuma da ya je ƙofar gidan ya kira shi a waya ya sanar da shi yana dakon fitowarsa, sai wasu ’yan daba suka afka masa inda suka soke shi a ƙirji abin da ya yi ajalinsa.

Ya ƙara da cewa sun je ofishin ’yan sanda na Bachirawa inda suka taho ƙafa da ƙafa da DPO domin bincike, amma abin bai yiwu ba, domin Dan Isle ya kwashe iyalinsa ya gudu daga unguwar, ya rufe gidansa, a cewar Abubakar.

’Yan uwan marigayin sun nemi hukumomi su yi bincike na adalci a kan lamarin.

Dangane da wannan alʼamari dai Arewa Updates ta yi ta kiran wayar Dan Isle amma wayarsa na nuna ʼbusyʼ, sai dai mun aika masa da saƙon kar-ta-kwana amma shiru babu amsa.

To amma muna ci gaba da jira, in ya magantu za mu sanar muku.

Ko a watan Mayun da ya wuce dai, Kansilan Mazabar Gobirawa a Dala, Hon. Ibrahim Danwaire, ya zargi Shugaban Karamar Hukumar Dala, Hon. Surajo Ibrahim Imam, da shirya masa wata kitimurmura inda aka lakada masa dukan tsiya a sakatariyar karamar hukumar, sai da kyar ya sha.

Sai dai shugaban karamar hukumar ya musanta wannan zargin. Inji Arewa Update.

punch news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp