Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a makarantar Faudiya Islamiyya da ke karamar hukumar Geidam a jihar Yobe da sanyin safiyar Juma’a, inda suka kashe dalibai uku, a cewar rundunar ‘yan sandan jihar Yobe.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar harin da misalin karfe 3:45 na safe.
A cewar sanarwar, maharan wadanda suka isa kan babura dauke da muggan makamai, sun mamaye makarantar ne da niyyar sace daliban.
Duk da haka, sun yanke shawarar kashe daliban nan da nan don guje wa “nauyin” kai su cikin daji.
Wani dalibi da ya yi yunkurin tserewa ya samu raunuka kuma an kai shi asibiti domin yi masa magani.
“An tabbatar; hedkwatar ‘yan sanda reshen Geidam ta samu rahoton da safiyar yau ta bakin wani mutum cewa an kai hari a wata makaranta.
“Mun tattara mutanenmu, kuma suka je can suka kwashe gawawwakin mutane uku da daya mai raunin harsashi wanda aka kwantar da shi a asibiti,” Abdulkarim ya shaida wa manema labarai.
Ya ci gaba da bayanin cewa, “Maharani sun zo ne a kan babura, kimanin 10 daga cikinsu, dauke da muggan makamai irin su AK-47 da sauran kayayyaki.
“Sun shiga makarantar ne suka dauki hudu daga cikin daliban, inda nan take suka kashe uku sannan suka raunata mutum daya.”
A cewar Abdulkarim, daya daga cikin daliban da suka samu raunuka ya bayyana cewa maharan sun shaida musu cewa sun yi niyyar sace su amma sun yanke shawarar kashe su a maimakon haka don gujewa matsalar safarar su.
Ya bayyana cewa a halin yanzu ‘yan sanda na gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gano musabbabin harin.