fidelitybank

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da mata da ƴar Kwamishina

Date:

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da matar da diyar Kwamishinan Muhalli na Jihar Filato, Idi Bamaiyi.

Majiyoyin iyalan sun shaida wa gidan talabijin na Channels cewa, an yi garkuwa da uwa da ‘yarta a safiyar ranar Asabar lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki gidan kwamishinan.

Sai dai sun tabbatar da cewa, an kai rahoton faruwar lamarin ga jami’an tsaro a kokarinsu na ganin an dawo da wadanda abin ya shafa.

An ce maharan sun shiga gidan ne da sanyin safiya kafin su yi awon gaba da mutanen a garin Gindiri da ke karamar hukumar Mangu ta jihar.

A cewar shaidun gani da ido, harin ya dauki kimanin sa’a guda ne yayin da ‘yan bindigar suka tare wasu manyan tituna a cikin garin yayin da ake ci gaba da kai farmakin.

Garin na Gindiri da kewaye dai na fuskantar hare-hare daga wasu ‘yan bindiga a cikin ‘yan makonnin da suka gabata inda aka yi awon gaba da wasu mazauna garin.

asuu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Zan cigaba da sa yawan jini ga maƙiya Tinubu – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya sha alwashin...

Tinubu zai magantu a kan ranar Dimokradiyya

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi jawabi ga...

A shirye nake na mutu don nasarar APC a 2027 – Orji Kalu

Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana...

Bayan hutun Sallah Tinubu zai koma Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu na kan hanyarsa ta komawa...

Mutane 570 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilu – Rahoto

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce, adadin...

PDP ba za ta mutu ba duk da rikicin cikin gida – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce...

Sojoji sun kashe riƙaƙen ɗan bindiga Guddel a Kaduna

Sojoji sun yi nasarar kawar da fitaccen shugaban ‘yan...

Fadar shugaban ƙasa ta yi kakkausar gargaɗi a kan Ndume

Fadar shugaban kasa ta yi kakkausar gargadi ga dan...

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...
X whatsapp