Ƴanbindiga sun tare da ƙwace kayayyakin abinci da na sha da wani mutum ya sayo a kan babur a garin Gidan Abe da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.
Wani dattijon garin ne ya tabbatar wa jaridar Daily Trust hakan, inda ya ce lamarin ya auku ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe biyar 5:23 na yamma.
“Mutumin ya tafi sayo buhun shinkafa da sauran kayan abinci domin bikin Kirsimeti a garin Katari. Da yake dawowa ne a hanyarsa ta zuwa gida sai wasu ƴanbindiga a kan babura suka tare shi, suka ƙwace.”
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴansandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur bai kai ga nasara ba.