Wasu da ake zargin ƴan bindiga sun toshe babbar hanyar Gusau zuwa Funtua mai cike da cunkoso tare da yin awon gaba da matafiya da dama.
Ƴan bindigar sun tare babbar hanyar da ke tsakanin al’ummar Kucheri da Magazu a karamar hukumar Tsafe, inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi.
Mai magana da yawun ƴansandan jihar ta Zamfara, ASP Yazid Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels, ya ce an yi garkuwa da mutanen da ba a tantance adadinsu ba a harin.
Ya ce jami’an tsaro na can suna hoɓɓasa don ganin an ceto mutanen da aka tafi da su.
“Lamarin ya faru ne da yammacin jiya Asabar. Ƴan bindigar sun tare hanya suka fara harbin kan masu tafiya inda suka yi garkuwa da wasu daga cikinsu,” inji kakakin ƴansandan.
Ya ce jami’ansu tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro suna aiki tare don ganin an ceto waɗanda aka sace.
Sai dai Abubakar ya musanta rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da ‘yansanda biyar a lokacin da suke artabu da ‘yan bindigar.
Zamfara dai na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren gungun ‘yan bindiga, waɗanda ke yin garkuwa da jama’a domin neman kuɗin fansa.