Wasu ‘yan bindiga sun kashe malami daya tilo a Unguwan Dorowa Bakhira a unguwar Maro da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
‘Yan bindigar sun kuma kashe wasu ma’aurata yayin harin da aka kai wa al’ummar, wanda ya faru da sanyin safiyar Lahadi.
Malamin makarantar firamare mai suna Mista Sunday Akor dan jihar Benue ne.
A cewar wani shugaban al’umma, Maigari Ben, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, babu wanda aka yi garkuwa da shi yayin harin.
Ya bayyana cewa, “Sun kashe wani mutum ne da matarsa da kuma wani malamin makarantar firamare, Mista Sunday Akor, wanda dan jihar Binuwai ne. Shi kadai ne malamin aji a makarantar firamare a kauyen nan. Babu wanda aka sace.”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya kasa samun jin ta bakinsa har zuwa lokacin hada wannan rahoto.