Wasu gungun ‘yan bindiga a safiyar yau Alhamis sun kai hari a karamar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar Anambra.
An banka wa sakatariyar wuta. Har yanzu ba a tabbatar da ko wani ya mutu ko ya jikkata ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta ce “Wani lamari ne da ake zargi da konewa”.
DSP Tochukwu Ikenga ya shaida wa manema labarai cewa, har yanzu bayanan suna cikin tsari.
Kakakin ya kara da cewa, an kara tura jami’an tsaro zuwa yankin kuma an tuntubi hukumar kashe gobara.
Ana zargin kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ce, ta yi kone-konen.
A watan Janairu ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a Ezinifitte da ke karamar hukumar Nnewi ta Kudu. Harin ya yi sanadin mutuwar wasu mutane.