Wasu mazauna yankin Shiroro da ke jihar Neja sun ce, ƴanbindiga sun daɗe suna kai hari domin lalata layin wutar lantarki na Shiroro-Kaduna 330kV na ɗaya da na biyu.
Lalacewar layin lantarkin ne dai ya jefa mafi yawancin jihohin arewa cikin rashin wutar lantarki, lamarin da ya tsananta, har ya jefa mutanen jihohin cikin ƙunci.
Mazauna yankin sun bayya wa jaridar Daily Trust layin wutar ya taso ne daga dam ɗin Shiroro ya ratsa ta yankin Chiri, wanda ya daɗe yana fama da matsalar rashin tsaro a ƙaramar hukumar Munya, sannan ya bi Sarkin-Pawa da Kafin-Koro na ƙaramar hukumar Paikoro.
Wani basarake a yankin ya ce inda layin ya ratsa duk yanki da ƴanbindiga suke bi, wanda a cewarsa dole ma’aikatan kamfanin rarraba lantarki su sha wahalar zuwa gyara saboda fargabar ƴanbindigar za su iya kawo musu hari suna tsaka da aikin.