Wasu ‘yan bindiga a ranar Talata da yamma, sun harbe wani soja har lahira yayin da wasu uku suka samu raunuka, yayin musayar wuta a kauyen Akoti da ke kusa da garin Kagarko a jihar Kaduna.
Wani mazaunin unguwar mai suna Musa Arungo, wanda ya tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin, ya ce wani farar hula kuma ya samu rauni yayin artabun da ‘yan bindigar suka yi.
A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.
Ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shanu sama da 80 kuma suna wucewa ta kauyen Akpoti ne aka sanar da sojoji.
“Abin takaici, ‘yan bindigar sun kashe soja daya, suka raunata uku a yayin da ake aikin.
“Daya daga cikin mutanen kauyen ya samu harsashin bindigar da ‘yan bindigar suka yi masa, kuma a halin yanzu yana jinya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja (UATH) da ke Gwagwalada,” inji shi.
Shi ma Madaki na Janjala, Samaila Babangida, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa “daga bayanan da na samu a safiyar yau, sojoji sun fito daga Kaduna domin kwashe sojoji uku da suka jikkata da kuma gawar wanda aka kashe.”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Mohammed Jalige, bai amsa kiran waya da sakonnin tes da aka aika masa ba.