Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shahararren dan kasuwa a kauyen Gangarbi da ke karamar hukumar Rogo a jihar Kano, Alhaji Nasiru Na’ayya da sanyin safiyar ranar Litinin.
Wata majiya ta shaidawa DAILY POST cewa, masu garkuwan sun mamaye gidan mutumin ne da tsakar daren ranar Litinin.
A cewarsa, a lokacin da suka isa gidan dan kasuwar, ‘yan bindigar sun fara harbe-harbe ba da jimawa ba domin tsoratar da mutane.
Ya ci gaba da bayyana cewa, “Lokacin da mazauna yankin suka yi yunkurin hana ‘yan bindigar tafiya da wanda abin ya shafa, sun harbe mutum biyu, lamarin da ya kai ga mutuwar daya nan take, wani kuma ya samu rauni kuma a halin yanzu yana samun kulawa a asibiti.”