Akalla mutane bakwai ne ake fargabar sun mutu a wani hari da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai a shalkwatar rundunar ‘yan sanda da ke garin Zurmi, a karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
Rahotanni na cewa ‘yan bindigar sun kai wa Zurmi hari da yammacin ranar Lahadi, inda suka kashe mutane bakwai ciki har da dan sanda guda.
Babangida Zurmi, dan asalin garin, ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu bai yi magana da wani dan uwansa ba har zuwa karfe 9:45 na dare.
“Yayin da muke magana yanzu, ba zan iya tuntuɓar kowa a garin ba, lambobin su a kashe suke. Hakan na nufin har yanzu ‘yan fashin na nan a wajen. Muna bukatar taimako daga hukumomin da abin ya shafa,” inji Zumi.
Wata majiya daga yankin ta ce, ‘yan bindigar sun kai hari garin ne da nufin daukar fansa kan kisan da ‘yan banga suka yi wa mutane biyu a yankin.
A cewarsa, an kona shaguna da dama sannan an kuma kona hedikwatar ‘yan sanda da ke Zurmi.
A wani labarin kuma, wasu gungun ‘yan bindiga da ke aiki a karamar hukumar Maradun sun kashe mutane hudu tare da yin awon gaba da wasu da dama.
A cewar majiyoyi, mutane hudun sun mutu ne a lokacin da ‘yan bindigar suka bude wuta kan mutanen da ke share ciyayi a kan hanyar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce yana ci gaba da tattara bayanai kan harin na Zurmi.


