fidelitybank

Ƴan bani na iya ne suka bayar da sunan Maryam Shetty ba tare da sani na ba – Ganduje

Date:

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce, wasu ‘yan ba-ni-na-iya ne suka bayar da sunan Maryam Shetty don naɗa ta minista daga Kano, ba tare da saninsa ba.

Sai dai, ya ce shugaban ƙasa yana da damar naɗa mutanen da yake son tafiya da su a muƙaman ministoci daga jihohin ƙasar bisa la’akari da tsare-tsarensa da ƙwarewar mutanen da kuma sauran buƙatu.

A wata hira da ya yi da wasu kafofin yaɗa labarai ciki har da Freedom Radio ranar Asabar, tsohon gwamnan, wanda shi ne jagoran jam’iyyar a Kano, ya ce ba shi da cikakkiyar masaniya a kan Maryam Shetty, hasali ma ba su santa ba a matsayinsu na jagororin APC daga Kano.

Don haka ”ka ga ba mu da wani ma’auni da za mu ce za ta iya, ko ba za ta iya wannan aiki ba idan aka nemi shawararmu”.

Ganduje ya ce martanin da mutane suka yi ta bayyanawa a shafukan sada zumunta, shi ma ya taka rawa wajen ɗaukar matakin sauya sunan Dakta Maryam Shetty, bayan wasu sun riƙa nuna cewa ba za ta iya riƙe muƙamin minista a Najeriya ba kasancewar ba ta taɓa riƙe wani muƙamin gwamnati ba.

Shugaban na APC ya ce da haka ne labari ya je har wajen shugaban ƙasa, wanda ya kira Ganduje don jin shawararsa.

”Ya ce min ga fa abin da ke faruwa, shin kai ka bayar da sunanta? Sai na ce masa a’a sam sam, ba ni ba ne, ban ma sani ba, daga nan ya ce to ya ka gani? akwai buƙatar a canja?, sai na ce masa ƙwarai da gaske kuwa”, in ji tsohon gwamnan na Kano.

Ganduje ya ce muƙamin minista, matsayi ne da ke buƙatar dattaku da sani (ƙwarewa), sannan yana buƙatar taka muhimmiyar rawa wajen kafa gwamnati a siyasance.

”To idan ka auna waɗannan abubuwa kuwa, ai mu ya kamata a tambaya, in dai ana so a bayar da wakilci daga jihar Kano”, in ji shi.

Ya ce ko da wani can ya bayar da wata shawara, to ya kamata a tuntuɓe su , idan ya dace sai su ba da goyon baya.

Cire sunan Maryam Shetty daga jerin ministocin Shugaba Tinubu, kamar bayyana sunanta a cikin waɗanda za a naɗa tun farko, ya yi matuƙar janyo muhawara musamman a tsakanin matasa da matan ƙasar.

Da yawa suna cewa abin da aka yi ya nuna rashin dacewa da kuma hangen nesa.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...
X whatsapp