Majalisar Wakilai, a ranar Alhamis, ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kara daukar matakan ganin an sako ‘yan Najeriya 51 da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna da kuma wasu ‘yan Najeriya da ke hannun ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a sassa daban-daban na kasar.
Majalisar ta kuma shawarci Gwamnatin Tarayya da ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai hada kai da hukumomin tsaro, domin ganin an sako wadanda aka yi garkuwa da su a kasar, da nufin taimakawa iyalan wadanda abin ya shafa.
Shawarar ta biyo bayan kudirin da Bamidele Salam (PDP Osun) da Julius Ihonvere (APC Edo) da Mansur Manu Soro (APC Bauchi) da wasu mutane bakwai suka gabatar kan wadanda ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan suka kashe a sassa daban-daban na kasar nan.
A cewar ‘yan majalisar, idan har ba a yi wani abu ba don ganin an ceto wadanda aka yi garkuwa da su a fadin kasar, to ‘yan kasar za su rasa kwarin gwiwa ga gwamnatin wancan lokacin.
‘Yan majalisar sun lura cewa lamarin na iya karawa masu aikata laifuka kwarin gwiwa da kungiyoyi su kara kaimi wajen aikata laifuka.