Wani Babban Lauyan Najeriya (SAN), Yakubu Maikyau, ya zama shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) na 31.
An nada Maikyau a matsayin sabon shugaban NBA, bayan zaben hukumar da aka gudanar.
Shugaban kwamitin zaben wanda kuma SAN ne, Farfesa Ayodele Akintunde ne ya bayyana hakan, a ranar Lahadi a Abuja yayin da yake bayyana sakamakon zaben.
Maikyau wanda ya samu kuri’u 22, 342 ya lashe zaben, sai kuma dan uwansa SAN, Joe-Kyari Gadzama wanda ya samu kuri’u 10,842.
Mista Taidi Jonathan ya zo na uku da jimillar kuri’u 1,373.
Bayan sanarwar, ana sa ran Maikyau zai karbi ragamar shugabancin kungiyar daga hannun shugaban NBA mai barin gado, Olumide Akpata.