Ƙungiyar Gwamnonin jihohin ƙasar nan, sun sake yin watsi da yunkurin fara cire kudaden Paris Club da suka kai dala miliyan 418, daga asusun tarayya, domin biyan wasu ‘yan kwangila.
Kungiyar gwamnonin ta aika wa gwamnatin tarayya wata wasika, inda ta ce taɓa kudaden waɗanda suke ƙalubalantar batun a gaban kotu, karan tsaye ne ga kundin tsarin mulkin kasa.
A wata wasika da ta aikewa gwamnatin tarayya, ƙungiyar gwamnonin ta bayar da hujjar cewa, duk wani yunƙurin daukar matakan fara zaftare kudaden, sun saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa, tun da ana shari’a a kan maganar.
Ta ce, kuma tuni ma kotu Ƙoli ta fadi matsayinta a kan batun.
Shugaban ƙungiyar, kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya sanya hannu kan wasiƙar.
Sannan ƙungiyar gwamnonin na ganin lamunin da aka bayar tun da farko, wanda gwamnatin tarayya ta shiga tsakani, kuma ake maganar sake fara cire shi, an bayar da shi ne bisa kuskure ta hannun wasu ƴan kwangila.
Sai dai har yanzu gwamnati ba ta ce komai ba game da wasiƙar da ƙungiyar gwamnonin suka aike mata.


