fidelitybank

Ƙungiyar Ƙwadago da ta Lauyoyi sun yi tir da gwamnatin Tinubu na mayar da zanga-zanga laifi

Date:

Ƙungiyar Ƙwadago NLC da takwararta ta lauyoyi NBA sun gana, inda suka soki lamirin gwamnati na mayar da zanga-zanga laifi a Najeriya, sannan suka bayyana cewa cigaban ƙasa mai dorewa na ta’allaƙa ne da bin doka da oda a dukkan matakan gwamnati.

Wannan bayanin yana ƙunshe ne a wata sanarwa da NLC ta fitar a shafinta na X bayan tattaunawar da ƙungiyoyin biyu suka yi a hedkwatar NBA a ranar Alhamis 12 ga Satumba a Abuja.

Ganawar ta buɗe wani sabon babin haɗaka tsakanin ƙungiyoyin biyu na ƙwadago da lauyoyi kamar yadda sanarwar ta nuna, inda suka ƙuduri aniyar yin aiki tare domin tabbatar da doka da oda da adalci da samar da daidaito.

Ganawar na zuwa ne bayan ƙurar da ta tashi bayan kama Shugaban NLC Joe Ajaero ta fara lafawa, inda jami’an DSS suka kama shi domin amsa wasu tambayoyin a kan zargin alaƙa da ɗaukar nauyin ta’addanci, cin amanar ƙasar da zamba ta yanar gizo.

Ƙungiyoyin biyu sun yi Allah wadai da matakin na gwamnati, sannan suka yi kira da babbar murya a kan kare ƴancin ƴan ƙasar, wanda a cewarsu yana da matuƙar muhimmanci domin ƙara wa dimokuraɗiyya garɗi.

A ziyarar, Shugaban NLC ya nanata shirinsu na aiki da Ƙungiyar NBA domin tabbatar da kare ƴancin ƴan Najeriya, musamman ma’aikata.

A nasa jawabin, Afam Osigwe, sabon zaɓaɓɓen Shugaban NBA, ya bayyana cewa a shirye ƙungiyarsu take na aiki da NLC a duk abubuwan da suka shafi shari’a, kamar shawarwari da kuma kare ƴan ƙasa da suke marasa galihu kyauta a kotu.

Ya ce wannan ne ma ya sa ya sake dawo da ɓangaren kare mutum a kotu ajalan domin tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya na samun kariya a kotu ba tare da la’akari da ƙarfin aljihunsa ba.

vanguard news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp