Ƙasashe 58 daga cikin 164 mambobin Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO) sun nuna goyon bayansu ga buƙatar neman shugabar ƙungiyar Ngozi Okonjo-Iweala ta yi tazarce wa’adi na biyu.
Ƙasashen sun bayyana goyon bayansu ne ga Okonjo-Iweala a babban taron ƙungiyar da aka gudanar ranar Litinin, kamar yadda WTO ke shirin tallafawa Intanet.
“Ƙungiyar Afirka da ake kira Africa Group ne ta gabatar da buƙatar cewa shugabar a shirye take ta yi wa’adi na biyu, kuma ta gabatar da buƙatar cewa a fara bin matakai na sake zaɓar ta ba tare da ɓata lokaci ba,” a cewar sanarwar.
Mambobin ƙungiyar 58 sun bayyana goyon bayansu ga Okonjo-Iweala a babban taron na WTO tare da yin kira ta fito ta bayyana aniyarta ta neman wa’adi na biyu.
Ƙasashen sun jinjina wa shugabar kan nasarorinta da kuma jajircewarta a wa’adinta na farko.
Okonjo-Iweala ta ce ta saurari buƙatar ƙasashen kuma za ta yi nazari game da buƙatar.
Okonjo-Iweala ƴar Najeriya, ita ce ta bakwai a matsayin shugabar WTO. Ta karɓi rantsuwar kama aiki ne a ranar 1 ga Maris a wa’adin farko na shekara huɗu kuma wa’adin zai ƙare ne a ranar 31 ga Agustan 2025.
Tsohuwar ministar kuɗi ta Najeriya ta kasance mace ta farko kuma ƴar Afirka da ta taɓa rike muƙamin shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya. In ji BBC.


