fidelitybank

Ƙarancin wutar lantarki ya sanya minista taron gaggawa a Najeriya

Date:

Ministan harkokin lantarkin, Inijiniya Abubakar D. Aliyu, ya kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki, domin samar da mafita dangane da matsalar wutar lantarkin Najeriya.

Taron ya kunshi kamfanonin samar da wutar lantarki da kuma hukumomi na gwamnati da masu zaman kansu da suke da ruwa da tsaki a harkar samar da wutar lantarki da iskar gas.

Taron, wanda aka gudanar a Abuja, Injiya Abubakar D. Aliyu ya ce, gwamnati ba za ta amince ba da yadda lamarin wutar lantarki ya samu koma baya, ya na mai cewa, dole a samo mafita ga dukkan matsalolin da suke kawo koma baya ga yawan wutar lantarki da ‘yan Najeriya suke samu a kullum.

Ministan ya kuma gargadi hukumomi da kamfanoni na harkar wutar lantarki su guji nunawa juna yatsa, su mayar da hankali wajen tallafawa juna wajen tabbatar da cewa ‘yan Najeriya suna samun isasshiyar wutar lantarki.

Taron ya mayar da hankali ne ga duba dukkan matsalolin da suke kawo koma baya ga harkar wutar lantarki a Nijeriya.

Injiniya Abubakar D. Aliyu ya ce, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, za ta ci gaba da kokarin daukar matakai, domin ganin cewa an samu karuwar wutar lantarkin da ake samarwa a Najeriya. In ji BBC.

nigeria newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp