Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce, kokarin da shugabanni baya da suka yi musamman wadanda suka yi gwagwarmaya a jamhuriya ta farko, ya gaza wajen hada kan ‘yan Najeriya.
Jonathan na wadannan kalamai ne a wani taro da aka gudanar a Abuja domin tunawa da marigayi Keftin Hosa Okunbo, a cewar jaridar Daily Trust ta Najeriya.
Tsohon shugaban ya ce shugabanni wannan zamanin sun gaji kasar ne cikin wani yanayi na rarrabuwa tsakanin yankunan uku da suka koma hudu daga baya.
Ya ce duk da irin kokarin da ake yi wajen sake gina kasa ta fuskar ci gaba da tattalin arziki akwai matsalolin kabilance da ke sake mayar da hannun agogo baya.
Tsohon shugaban Najeriya, ya ce akwai jan aiki a gaba saboda batu kabilanci abu ne da shugabanni baya ba su kawar ba, don haka a wannan lokaci aiki da irin wannan akida da kamar wuya.
Shi ma a lokacin na shi tsokacin tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole ya ce ‘yan Najeriya ba sa yaban shugabanninsu har sai sun sauka daga mulki.


