Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ziyarci birnin Kherson kwanaki bayan dakarunsa sun ƙwato birnin daga hannun sojojin Rasha.
Ya kuma yi jawabi ga dakarun da suka taru a birnin inda ya bayyana cewa ƙasarsa na samun ci gaba, kuma a shirye take domin samun zaman lafiya.
Ƙwace birnin Kherson, wanda ke hannun Rasha tun farkon mayayar, wani babban koma-baya ne ga ƙasar ta Rasha.
A baya dai Rasha ta bayyana birnin a matsayin cibiyar mulkin yankin da ta kwace tun farkon mamayar.
Dakarun Ukraine sun shiga birnin a ranar Juma’a, karon farko tun cikin watan Maris.
A ‘yan kwanakin nan dai an yi ta ganin mazauna birnin na ta murna sakamakon sake ganin juna da suka yi karon farko cikin watanni.
Mista Zelensky ya gode wa ƙungiyar tsaro ta NATO da sauran ƙawayensa saboda goyon baya da suka bai wa ƙasarsa a lokacin yaƙin.