Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine, ya nemi hadin kai tsakanin kasashen Turai domin mayar da martani mai karfi kan amfani da makashi da Rasha ke yi a matsayin makamin yaki.
A jawabinsa kwana ɗaya bayan gwamnatin Rasha ta ce ba za ta sake komawa kan batun ci gaba da tura musu gas ba, Mista Zelensky ya ce Rasha na amfani da wannan damar domin matsa wa Turai lamba kan makamashi ta hanyar yi musu barazana a inda suke da rauni.
Jami’an Tarayyar Turai sun ce a shirye suke su fuskanci kowane irin yanayi ba tare da dogara kan gas din Rasha ba idan aka kai wani mataki.
Sai dai tsadar da gas din ya yi a daidai lokacin da ake shirin shiga lokacin hunturu na ɗaga hankulan al’umma a Turai. In ji BBC.


