fidelitybank

Zauren hadin kan Malamai da kungiyoyin addini sun roki KAROTA da ‘yan Adaidaita

Date:

Zauren Hadin Kan Malamai da Kungiyoyin Addinin Musulunci a Jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin Jihar da kungiyar direbobin babur mai kafa uku da a ka fi sani da A daidaita Sahu da su sasanta tsakaninsu.

Kiran na zuwa ne a daidai lokacin da yajin aiki direbobin babur din suka fara a Jihar ranar Litinin ya shiga yini na uku.

Cikin zantawa da manema labarai, sakataren Zauren, Dr, Sa’id Ahmad Dukawa ne ya tabbatar da hakan..

Ya ce”Zauren ya damu matuka da halin yajin aikin, matuka baburan ya jefa al’ummar Jihar cikin kangi.

A cewarsa, “Kasancewar wannan yajin aikin ya shafi zirga-zirgar ’yan makaranta da ma’aikata da ’yan kasuwa da marasa lafiya masu zuwa asibiti da sauran al’ummar gari masu bukatu daban-daban, Zauren ya damu matuka da irin hali da al’umma suka shiga a sanadiyyar yajin aikin, musamman duba da yanayin da dama ake ciki na kunci da matsin halin rayuwa.A dalilin hakan, Zaure yana kira ga gwamnati da matuka baburan da su yi la’akari da yanayin da dubban mutane suka fada, su gaggauta zama tare don bibiyar matsalolinsu tare da warware su cikin ruwan sanyi.”

Zauren ya kuma jaddada rokonsa ga bangarorin biyu da su dubi Allah tare da duba halin da al’umma ke ciki na rashin abin hawa a Kano.

vanguardnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...
X whatsapp