fidelitybank

Yunwa: Dokar hana fita ta fara aiki a Darfur

Date:

Hukumomi a jihar Darfur ta Arewacin kasar Sudan sun sanar da kafa dokar hana fita da daddare a ranar Laraba bayan da wasu kungiyoyi dauke da makamai su ka yi awon gaba da wani rumbun adana kayan abinci na Majalisar Dinkin Duniya da kayayyakin da wata tsohuwar tawagar wanzar da zaman lafiya ke amfani da ita.

A cewar rahotannin farko na Majalisar Dinkin Duniya da ta fitar cewa, rumbun ajiyar kayayyaki da ke El Fasher da wasu kungiyoyi dauke da makamai su ka wawashe a yammacin ranar Talatar da ta gabata, na kunshe da ton 1,900 na abinci da a ka tanada, domin dubban daruruwan mutane a yankin.

Rikici da kone-kone ya lalata shagunan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na SUNA ya ruwaito. A ranar Laraba, an ji karar harbe-harbe a kusa da wurin ajiyar rumbin abincin, kamar yadda wani mazaunin garin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

“Daya daga cikin mutane uku a Sudan na bukatar agajin jin kai. Irin wannan harin ya na matukar kawo cikas ga iya kai ga mutanen da suka fi bukata,” inji jami’ar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya Khardiata Lo N’diaye.

vanguard 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Makami mai Linzami ya faÉ—a kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta Æ™addamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo Æ™arshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar Æ´ansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin Æ´an Æ™asarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a Æ™yale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maÆ™ale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi É—an shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...
X whatsapp