fidelitybank

Yarjejeniyar Isra’ila da Hamas za ta fara aiki ranar Lahadi

Date:

Majalisar ministocin Isra’ila ta kammala amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, wadda ta ƙunshi musayar waɗanda Hamas ke garkuwa da su da kuma sakin fursunoni Falasɗinawa da ake riƙe da su a Isra’ila.

Matakin na zuwa ne bayan shafe sa’o’i ana tattaunawa har zuwa cikin tsakiyar dare.

Ɗaya daga cikin ministoci masu tsattsauran ra’ayi ya ce zai ajiye muƙaminsa domin nuna adawa da batun, yayin da ɗaya kuma ya ce shi ma zai fice daga gwamnatin idan ba a ci gaba da yaƙin ba bayan ƙarewar matakin farko na yarjejeniyar, wanda zai ƙare cikin mako shida.

Yarjejeniyar za ta fara aiki ne a gobe Lahadai.

Da farko za a saki mutum uku da Hamas ke garkuwa da su yayin da ita kuma Isra’ila za ta saki Falasɗinawa fursunoni da take tsare da su.

Haka nan Isra’ila za ta fara janye dakarunta daga Gaza.

vanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...
X whatsapp