‘Yan wasan Manchester United sun dawo daga kasar Moldova, inda suka kara da FC Sheriff a gasar cin kofin Europa a ranar Alhamis din da ta gabata wanda aka bayyana cewa ‘yan wasan sun ci gubar abinci, in ji jaridar UK Sun.
United ta samu nasara ne da ci 2-0 a balaguron farko da suka yi a kasar da ke gabashin Turai.
Kwallayen da Jadon Sancho da Cristiano Ronaldo suka zura a farkon rabin farko ya sanya kungiyar Erik ten Hag ta farfado daga rashin nasara da suka yi da Real Sociedad a gasar.
Sai dai kuma yanzu haka ya bayyana cewa, akalla ‘yan wasan 12 ne suka fara jinya bayan dawowar su da safiyar Juma’a.
United dai ta koma Birtaniya ne a wani jirgin sama mai zaman kansa bayan wasan, amma duk da haka ta kamu da wata cuta da ba a san ta ba, wadda ake kyautata zaton ta fito ne daga wani abu da suka ci, ko kuma daga jirgin da kansa.
Wasu Æ´an wasan sun rasa horon da aka shirya gudanarwa a ranar Juma’a a Carrington, yayin da wasu ke fama da rashin lafiya a washegari.
Godiya ga Ten Hag, ba dole ba ne ya shirya kungiyar don wasan gida da Leeds United, wanda aka shirya yi tun ranar Lahadi.
An dage wasan ne saboda karancin ‘yan sanda kafin jana’izar Sarauniyar a ranar Litinin a Westminster Abbey.


