Rundunar ‘yan sandan jihar Filato, ta gurfanar da Moses Okoh, mai shekaru 20, wanda a ke zargin ya kashe Jennifer Anthony, daliba mai matakin ajin level 300 na Jami’ar Jos (UNIJOS), wadda a ka tsinci gawarta a ranar 1 ga watan Janairu, a wani gidan baki a Jos.
Okoh wanda a ke zargin saurayinta ne ya gudu, bayan ya aikata laifin. Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Bartholomew Nnamdi Onyeka, a cikin jawabinsa na farko ga manema labarai, ya gabatar da wanda a ke zargin da sauran masu aikata laifuka, inda ya haddasa barna, kashe-kashe da kuma yin garkuwa da mutane a jihar.
CP ya bayyana cewa, rundunar ‘yan sandan a yunkurinta na cafke Okoh, ta kaddamar da farautarsa tare da bibiyar shi da dabara zuwa jihar Benuwe inda ‘yan sanda su ka kama shi.
Ya ce”Za a gurfanar da wanda a ke zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike”.
Wanda a ke zargin an daure shi a bayansa da duk wani farin kyalle mai cike da jini wanda a ka yi amfani da shi wajen fizge idanuwa Jennifer, magunguna da kayan da a ka yi amfani da su wajen gudanar da aikin sa a yayin holonsa.