Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan banga, sun cafke wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Ringim da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a garin Dutse ranar Lahadi.
Shiisu ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar Alhamis bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki kan maboyarsu a kauyen Nisan Marke.
Ya ce wadanda ake zargin sun yi garkuwa da wani mai suna Muhammad Sama’ila mai shekaru 45 daga kauyen Madari da ke karamar hukumar Warawa a jihar Kano.
“A ranar 24 ga Agusta, 2022, da misalin karfe 8 na safe, bayanan sirri da muka samu sun nuna cewa, an ga wani Muhammad Sama’ila mai shekaru 45 a kauyen Madari, karamar hukumar Warawa, ta jihar Kano, an yanke masa karan a jikin sa.


