Mazauna garin Zugu na Ƙaramar Hukumar Bukuyum a Jihar Zamfara, sun wuni cikin tashin hankali, bayan ‘yan fashi ɗauke da mugayen makamai sun kutsa masallacin Juma’a ‘yan mintuna kafin tayar da sallar.
Bayanan da BBC Hausa ta tattara sun nuna cewa, maharan sun shiga masallacin tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 1:30 na rana kuma suka yi awon gaba da mutane da dama.
Kazalika, sun wuce zuwa kasuwar da ke garin inda a nan ma suka tafi da wasu. Jimilla, mutum aƙalla 44 ake zaton sun sace.
Wani mazaunin yankin ya ce baya ga mutanen da suka sace, ‘yan fashin sun kuma ɗebi kayayyakin abinci da sauran abubuwa.
Rundunar ‘yan sandan Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce ba ta da haƙiƙanin adadin mutanen da aka sace ɗin.
“Sun ɗebi kayan abinci kamar biredi da wayoyin mutane da batira,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu wani bayani da suka samu daga jami’an tsaro ko kuma ‘yan bindigar.


