Hukumar Lafiya ta Duniya, (WHO) ta bayar da dama ta gaggawa, domin samar da wata karin allurar riga-kafin cutar korona, mai suna Covovox, domin amfanin musamman kasashe matalauta.
Cibiya mafi girma da ke samar da riga-kafi a duniya, Serum Institute da ke Indiya, ita ce za ta samar da maganin karkashin ikon kamfanin Amurka Novavax.
Yanayin da duniya ta tsinci kanta a ciki a wannan lokacin inda ake ta samun karuwar masu kamuwa da cutar korona a kasashen duniya masu arziki da yawa, a sanadiyyar sabon nau’in cutar, wato Omicron, shi ne ya sa duniya ta shiga taitayinta da cewa ba wanda zai tsira idan ba kowa da kowa ya tsira ba.
Daman tun kafin a zo wannan gaba, da jimawa Hukumar lafiya ta Duniya take ta jaddada bukatar ganin an samar da isasshen riga-kafin da za a yi wa mutane a kasashe matalauta domin a gudu tare a tsira tare, amma WHO ta damu da yadda kasashe masu arziki maimakon su tabbatar da samar da wadatacciyar allurar a kasashe matalautan, sai suka rika tarawa fiye da bukatarsu wai domin gaba. A cewar BBC.